Kashe makudan kudade na bata mana gasa — Wenger

Makudan kudaden da kulob-kulob suke kashewa ne yake bata mana gasa. Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Makudan kudaden da kulob-kulob suke kashewa ne yake bata mana gasa.

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce, kungiyoyin da suke kashe makudan kudade ne suke bata manyan gasar League biyar na Turai.

Dan kasar Faransan ya buga misali da Faransa, da Jamus, da Ingila da kuma Spaniya.

Paris St-Germain ta bayar da tazarar maki 11 a gasar Ligue 1, Bayern Munich ta bayar da tazarar maki 16 a gasar Bundesliga, Manchester City ma tayi fintikau da maki 15 a teburin Firimiya.

Wadannan kungiyoyi suna daga wadanda suka fi kashe kudi a kasashen su.

hakan ta sa Wenger ya ce "makudan kudaden da kulob-kulob suke kashewa ne yake bata mana gasa."

A ranar da za a rufe kasuwar 'yan kwallo ranar Laraba ma fam miliyan 150 aka kashe, inda jimilla aka batar da fam miliyan 450 a watan Janairun.

Labarai masu alaka