West Ham ta kori Tony Henry bisa batanci ga 'yan Africa

"Kwarewar dan kwallo muke dubawa, ba ruwanmu daga inda ya fito". In ji kocin. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption "Kwarewar dan kwallo muke dubawa, ba ruwanmu daga inda ya fito". In ji kocin kungiyar.

West Ham ta kori daraktan daukar 'yan kwallo Tony Henry akan ikirarin da ya yi na cewa,' kulob din ba zai sake daukar 'yan kwallon Afirka ba".

Matakin ya biyo bayan rahoton da jaridar Daily Mail ta wallafa, inda ta rawaito Henry yana cewa,"Yan kwallon Afirka na haddasa yamutsi idan ba sa cikin kungiya".

Kulob din ya ce kalaman nasa sun saba ka'ida, kuma ba za a amince da nuna kowace irin wariya ba.

Kocin kungiyar David Moyes ya ce sun yi kokarin daukar 'yan Afirka biyu Islam Slimani da Ibrahim Amadou kafin a rufe kasuwar ranar Laraba.

"Kwarewar dan kwallo muke dubawa, ba ruwanmu da inda ya fito". In ji kocin.