Ina nan daram a Chelsea-Conte

Chelsea ce ta shida a teburin gasar Firimiya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Chelsea ce ta shida a teburin gasar Firimiya Chelsea ce ta shida a teburin gasar Firimiya

Kocin Cheasea Antonio Conte ya ce,"ya daura aniyar ci gaba da aikin horor da kungiyar har zuwa wata 18 lokacin da kwantiraginsa zai kare.

Dan kasar Italiyan ne yake jan ragamar kungiyar tun daga shekarar 2016, wanda ya kai ta ga nasarar lashe kofin Firimiya a kakarsa ta farko.

Yanzu Chelsea ce ta shida a teburin gasar Firimiya da tazarar maki 18 tsakaninta da ta daya a teburin Manchester City.

Ya ce,"Abun da nake so na fada muku yanzu shi ne har yanzu ina da sauran kwantiragi ta wata 18 tsakanina da Chelsea, kuma na dau aniyar mutunta yarjejeniya".

"Mun kula yarjejeniyar shekara uku. Kuma ina ganin muradinmu shi ne ci gaba da aiki tare". In ji kocin.