Batshuayi ya ci wa Dortmund kwallo biyu

Dortmund Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Batshuayi zai buga wa Dortmund wasannin aro zuwa karshen kakar bana

Dan wasan Chelsea, Michy Batshuayi ya ci kwallo biyu a wasan farko da ya buga wa Borussia Dortmund a gasar Bundesliga da ta je ta ci FC Koln 3-2 a ranar Juma'a.

Batshuayi wande ke buga wa Dortmund wasanni aro ya ci kwallon farko tun kafin aje hutu, bayan da aka dawo ya kara na biyu.

Simon Ziller da Jorge Mere ne suka ci wa Koln kwallaye, daga baya Batshuayi ya bai wa Andre Schurrle kwallon da ya ci na uku a karawar.

Da wannan sakamakon ya sa Dortmund ta koma ta biyu a kan teburin Bundesliga.

Labarai masu alaka