Arsenal ta sharara kwallaye a ragar Everton

Arsenal Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Arsenal tana ta shida a kan teburin Premier da maki 45

Arsenal ta yi nasarar cin Everton kwallo 5-1 a gasar Premier wasan mako na 26 da suka fafata a ranar Asabar a Emirates.

Tun kafin aje hutu Arsenal ta ci kwallo hudu ta hannun Ramsey da ya ci biyu da wadda Koscielny ya ci, sannan sabon dan wasan Gunners, Aubameyang ya ci na hudu.

Bayan da aka dawo ne daga hutu Calvert-Lewin ya ci wa Evrton kwallo, daga baya Ramsey ya ci na biyar kuma na uku a fafatawar.

Da wannan sakamakon Arsenal ta ci Everton kwallo sama da 100, kuma babu wata kungiya da Gunners ke yi wa ruwan kwallaye kamar Everton.

Kocin Everton, Sam Allardyce ya ja ragamar wasan Premier na 500 a kungiyoyin da ya horar, kuma shi ne na biyar da ya taka wannan tsanin.

Arsene Wenger ya ci karawa ta 500 a Premier, yayin da Harry Rednaff ya yi canjaras, shi kuwa David Moyes da Sir Alex Ferguson kashi suka sha.

Labarai masu alaka