Real Madrid ta yi canjaras shida a La Ligar bana

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kocin Real Madrid, Zinedine Zidane na kara shiga matsi a wasannin da yake jan ragama

Kocin Real Madrid, Zinedine Zidane ya ce ya yi bakin ciki da Levante ta farke kwallo daf da za su tashi a wasan La Liga a ranar Asabar.

Kungiyoyin biyu sun buga 2-2, kuma tun farko Real ce ta fara cin kwallo ta hannun Sergio Ramos a minti na 11 da fata wasa, yayin da Emmanuel Boateng ya farke wa Levante.

Isco ne ya ci wa Madrid kwallo na biyu saura minti tara a tashi daga fafatawar, sai dai Levante ta farke daf da alkalin wasa zai tashi karawar.

Real Madrid mai rike da kofin La Liga na bara tana mataki na hudu a kan teburin gasar, tazarar maki 18 tsakaninta da Barcelona ta daya, wadda za ta kara da Espanyol a ranar Lahadi.

Wannan shi ne karo na shida da Real ta tashi canjaras a gasar La Liga ta bana.

Labarai masu alaka