Dambatawar Shagon Mada da Dogon Bunza

Dambatawar Shagon Mada da Dogon Bunza

Dambe 11 aka yi a ranar Lahadi a gidan wasa na Ali Zuma da ke unguwar Dei-Dei a safiyar Lahadi a Abuja, Nigeria.

Dambe 11 aka yi a ranar Lahadi a gidan wasa na Ali Zuma da ke unguwar Dei-Dei a safiyar Lahadi a Abuja, Nigeria.

Ga rahoton da Mohammed Abdu ya hada mana

An fara da wasan da Shagon Shagon Lawwalin Gusai daga Arewa ya buge Bahagon Ebola daga Kudu a turmin farko, daga nan aka yi karawa tsakanin Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa da Shagon Isuhun Fandam daga Kudu babu kisa, haka ma wasan Bahagon Gambo daga Kudu da Tetenus din Na Bacirawa daga Arewa babu wanda ya je kasa.

Shi kuwa John Sina daga Arewa buge Bala Shagon Kwarkwada daga Kudu ya yi a turmin farko, sai dai karawa tsakanin Shagon Autan Faya daga Kudu da Autan Na Dutesn Mari Guramada canjaras suka yi.

Kurarin Kwarkwada daga Kudu kuwa buge Nuran Dogon Sani daga Arewa ya yi, karawa tsakanin Dogon Bahagon Sisco daga Kudu da Fafa daga Arewa turmi daya suka yi babu kisa.

Shagon Mada daga Kudu da Dogon Bunza daga Arewa turmi biyu suka yi aka raba su, Garkuwan Mahautan Jere daga Arewa buge Dan Shariff daga Kudu ya yi, yayin da aka yi turmi uku babu kisa tsakanin Shagon Fanteka daga Kudu da Tetenus din Na Bacirawa daga Arewa.

Wasan karshe an yi ne babu kisa tsakanin Shagon Autan Faya daga Kudu da Shagon Salisi daga Arewa.