Barca ta yi wasan La Liga 22 ba a doke ta ba

Barcelona Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Barcelona ta ci gaba da zama a mataki na daya a kan teburin La Liga

Kungiyar Barcelona ta tashi wasa 1-1 da Espanyol a gasar cin Kofin La Liga wasan mako na 22 da suka kara a ranar Lahadi.

Gerard Moreno ne ya fara ci wa Espanyol kwallo, bayan da aka koma daga hutun rabin lokaci.

Barcelona ta farke ta hannun Gerrard Pique saura minti takwas a tashi daga fafatawar.

Wannan sakamakon na nufin Barcelona ta yi wasa 22 a gasar ta La Ligar bana, ba tare da an doke taba.

Kocin Barcelona, Ernesto Valverde ya yi nasarar wasa 18 da canjaras hudu, sannan ya ci kwallo 60 aka zura 11 a ragar kungiyar da yake jagoranta a kakar nan.

Kungiyar da ke Camp Nou ta taba yin wasa 31 a gasar ba tare da an doke ta ba a 2010/11 karkashin Pep Guardiola tun daga mako na uku zuwa na 33.

Real Sociedad ce ke rike da tarihin wasa 32 ba a doke ta ba a La Liga da ta kafa a 1979/80.