An bai wa Di Biagio rikon kwaryar Italiya

Italia Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Di Biagio shi ne ya horar da tawagar kwallon kafar matasan Italiya 'yan shekara 21

Hukumar kwallon kafar Italiya ta nada Luigi Di Biagio a matsayin kocin tawagar kasar na rikon kwarya, domin ya ja ragamar wasannin sada zumuntar da za ta yi da Argentina da Ingila.

Mataimakin shugaban hukumar, Alessandro Costacurta, ya ce Italiya za ta iya bai wa kocin matasan kasar 'yan kasa da shekara 21 damar horar da babbar tawagar idan ya taka rawar gani.

Kocin mai shekara 46, wanda tsohon dan wasan Roma da Inter Milan ne, zai ja ragamar wasan sada zumuntar da Italiya za ta yi da Argentina a Ettihad a ranar 23 ga watan Maris.

A ranar 27 ga watan Maris kuma Italiya za ta kece-raini da Ingila a Wembley.

Italiya, wadda ta kasa samun tikitin shiga Gasar Kofin Duniya da za a yi a Rasha a bana, tana neman wanda zai maye gurbin Giampiero Ventura wanda ta raba gari da shi a watan Nuwamba.