Valencia za ta karbi bakuncin Barca a Copa del Rey

Barcerlona Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Barcelona ta buga wasan La Liga 22 a jere ba a doke ta ba a bana

Valencia za ta karbi bakuncin Barcelona a wasa na biyu a Copa del Rey a ranar Alhamis.

A wasan farko da kungiyoyin biyu suka fafata a Nou Camp ranar 1 ga watan Fabrairu, Barcelona ce ta ci daya mai ban haushi.

Barca na bukatar cin Valencia ko yin canjaras, inda hakan zai kai kungiyar wasan karshe na hudu a jere a Copa del Rey.

Haka kuma kungiyar wadda keda tarihin lashe kofin sau 30 jumulla, ta dauka sau uku a jere, inda take fatan zama ta daya da ta ci sau hudu a jere tun bayan farkon shekarar 1930.

Duk wadda ta yi nasara tsakanin Barcelona da Valencia, za ta fuskanci Sevilla ko Leganes a wasan karshe, wadan da suka tashi 1-1 a wasan farko na daf da karshe.