Ronaldo ya cika shekara 33 da haihuwa

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Real Madrid
Image caption Real Madrid tana fama da kalubale a kakar bana, inda take ta hudu a kan teburin La Liga

Dan wasan tawagar kwallon kafa ta Portugal mai taka-leda a Real Madrid, Cristiano Ronaldo ya cika shekara 33 da haihuwa.

An haifi Cristiano Ronaldo dos Santos Aveiro a ranar 5 ga watan Fabrairun 1985 a Funchal, Madeira, ta Portugal.

Ronaldo ya fara buga kwallo a Andorinha da Nacional da karamar kungiyar Sporting, sannan ya fara buga wa babbar kungiyar Sporting a shekarar 2002.

A shekarar 2003, Manchester United ta dauki dan wasan kan fam miliyan 12, inda ya yi mata wasa shekara shida a Old Trafford.

Ronaldo wanda ya yi wasa karkashin Sir Alex Ferguson ya ci kofin Premier uku da FA da League Cup da na Zakarun Turai, sannan ya lashe kyautar Ballon d'Or a 2008.

A shekarar 2009, Real Madrid ta sayi Ronaldo kan kudi fam miliyan 80 a matsayin mafi tsada a duniya a fagen kwallo kafa a tarihi.

A spaniya ne dan kwallon ya lashe kofin La Liga biyu da Copa del Rey biyu da kofin Zakarun Turai da lashe kyautar Ballon d'Or hudu a Real Madrid.

Ronaldo ya ci wa Madrid kwallo 426 a wasa 421, ciki har da 61 da ya ci a karawa 54 a kakar 2014/15.

Dan kwallon shi ne Kyaftin kuma kan gaba wajen buga wa Portugal wasa 147, inda ke na daya wajen ci mata kwallaye, bayan da ya ci 79, ya kuma lashe kofin nahiyar Turai a 2016.

Labarai masu alaka