Nasarawa ta samu maki uku a kan Yobe Stars

Nigeria Premier League
Bayanan hoto,

Nasarawa United za ta ziyarci Niger Tornadoes a wasan mako na takwas

Nasarawa United ta doke Yobe Stars da ci 3-0 a gasar Premier karashen wasan mako na bakwai da suka kara a ranar Litinin.

Abubakar Abdullahi ne ya fara cin kwallo a minti na 33, saura minti takwas a tafi hutu ne Zenke ya ci na biyu, bayan da aka dawo daga hutu Kabiru Balogun ya kara na uku a raga.

Da wannan sakamakon Nasarawa United ta koma ta 11 a kan teburi da maki tara, ita kuwa Yobe Stars tana ta tara da makinta 10 a kan teburin gasar.

Nasarawa United za ta ziyarci Niger Tornadoes a wasan mako na takwas a ranar 11 ga watan Fabrairu.