Deportivo ta nada Seedof sabon kocinta

Deportivo Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Seedof shi ne koci na uku da zai horar da Deportivo a kakar bana

Deportivo La Coruna ta nada Clarence Seedorf a matsayin sabon kociyanta, domin ya ja ragamar kungiyar zuwa karshen kakar bana.

Seedof tsohon dan kwallon tawagar Holand da kungiyar AC Milan da Real Madrid, zai maye gurbin Cristobal Parralo

A ranar Lahadi Deportivo ta sallami Parralo, bayan da Real Socidad ta doke ta 5-0 a ranar Juma'a.

Kungiyar tana ta 18 a kan teburin La Liga, kuma cikin dura mata kwallaye da aka yi har da 7-1 da Real Madrid ta ci ta da 4-0 da Barcelona ta yi nasara a kanta.

Labarai masu alaka