Conte zai ci gaba da horar da Chelsea

Chelsea Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Chel;sea tana ta hudu a kan teburin gasar Premier

Chelsea ba za ta sallami Antonio Conte ba, bayan da kungiyar ta sha kashi a hannun Watford da ci 4-1 a ranar Litinin.

Wata majiya ta kusa da Chelsea ta ce za ta ci gaba da aiki da Conte tunda kungiyar tana cikin 'yan hudun farko, sannan tana buga gasar Kofin Zakarun Turai da Kofin FA .

Kyaftin din Chelsea, Gary Cahill yana goyon bayan Conte, ya kuma bukaci 'yan wasa da su kalli rawar da suka taka a karawar da aka doke su a Watford.

Chelsea tana ta hudu a kan teburin Premier, kuma Manchester City wadda take ta daya a kan teburin ta ba ta tazarar maki 19.

Labarai masu alaka