Neymar ne kan gaba a karbar albashi a Faransa?

PSG Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption PSG ce ta daya a kan teburin Faransa

A karshen watan Janairu aka kammala cin kasuwar saye da sayar da 'yan kwallon kafa a wasu kasashen Turai.

Kasuwar gasar Ingila ce aka fi yin hada-hada mai tsoka daga cikin manyan wasannin da ake yi a Turai da ta hada da Spaniya da Bundesliga da Serie A da kuma Ligue 1.

Jaridar L'Equipe ta Faransa ta wallafa sunayen 'yan kwallon da suka fi daukar albashin mai tsoka a kowanne wata.

Ga jerin goma daga cikinsu. Duk Euro daya dai-dai da Naira 443.98, wato Naira 444.

  1. Neymar (PSG) €3.06m Naira Biliyan 1,358,640,000
  2. Edinson Cavani (PSG) €1.54m Naira Miliyan 683, 760,000
  3. Kylian Mbappe (PSG) €1.5m Naira Miliyan 666,000,000
  4. Thiago Silva (PSG) €1.33m Naira Miliyan 590,520,000
  5. Angel Di Maria (PSG) €1.12m Naira Miliyan 497,280,00
  6. Marquinhos (PSG) €1.12m Naira Miliyan 497,280,000
  7. Thiago Motta (PSG) €875,000 Naira Miliyan 388,500,000
  8. Javier Pastore (PSG) €770,000 Naira Miliyan 341,880,000
  9. Radamel Falcao (Monaco) €750,000 Naira Miliyan 333,000,000
  10. Dani Alves (PSG) €700,000 Naira Miliyan 310,800,000

Labarai masu alaka