Ronald Koeman ya zama kocin Holland

Holland Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Rabon da Koeman ya horar da tamaula tun cikin watan Oktoba

Hukumar kwallon kafa ta Holland ta nada Ronald Koeman a matsayin kocin tawagar kasar, kan yarjejeniyuar shekara hudu da rabi.

Rabon da Koeman mai shekara 54 ya horar da tamaula tun cikin watan Oktoba, bayan da Everton ta sallame shi.

Koeman zai maye gurbin Dick Advocaat wanda ya kasa kai Holland gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a bana.

Wannan ne aiki na 10 da Koeman zai yi a matsayin koci, bayan da ya horar da Vitesse Arnhem da Ajax da Benfica da PSV Eindhoven da Valencia da AZ Alkmaar da Feyenoord da Southampton da kuma Everton.

Koeman ya yi wa Holland wasa 78, yana daga cikin wadanda suka dauki kofin nahiyar Turai a shekarar 1988, a lokacin da kasar take da fitattun 'yan wasa da suka hada da Ruud Gullit da Frank Rijkaard da kuma Marco van Basten.

Haka kuma ya buga wa kungiyoyi da suka hada da Barcelona da Ajax da kuma PSV.