Luis Enrique zai maye gurbin Conte a Chelsea

Chelsea Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Enrique na yin hutu ne bayan da ya bar aikin horar da Barcelona

Tsohon kocin Barcelona, Luis Enrique yana daga cikin wadanda Roman Abramovich ke son bai wa aikin horar da Chelsea, idan ya kori Antonio Conte in ji Sport da Spaniyanci.

Le10Sport da harshen Faransanci ta ce da zarar an bai wa Enrique kocin Chelsea, zai fara da sayo dan kwallon Uruguay, Luis Suarez domin ya karawa kungiyar karfi.

Sai dai kuma Goal ta ce Enrique ba shi da niyar katse hutun shekara daya da yake yi, zai fi kaunar karbar aikin horar da tamaula idan an kammala wasannin bana.

Ita kuwa Talksports cewa ta yi Conte yana girbar kuskuren da tsohon daraktan tsare-tsare, Michael Emenalo ya yi a lokacin cinikayyar 'yan kwallo a bazara in ji tsohon dan wasan Chelsea Ray Wilkins.

Mirror ta wallafa cewar saura wata 18 yarjejeniyar Conte ya kare a Chelsea, kuma ba shi da niyyar yin murabus.

Abramovich ba zai taba yadda cewar 'yan wasa ne za su yanke makomar Conte ta ko ya ci gaba da zama a Stamford Bridge ko akasin hakan in ji Telegraph.

Labarai masu alaka