West Ham United ta dauki Patrice Evra

West Ham United Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Evra ya buga wa Manchester United tamaula da Juventus da Marseille

West ham United ta dauki tsohon dan wasan Manchester United, Patrice Evra kan yarjejeniyar karshen kakar bana.

Evra dan kwallon tawagar Faransa mai shekara 36, ba shi da kungiya tun bayan da ya raba gari da Marseille, sakamakon yi wa magoyin bayan kafa a lokacin gasar Europa.

Hukumar kwallon kafa ta Turai ta dakatar da shi buga wasannin gasar har zuwa karshen kakar shekarar nan, amma zai iya buga fafatawar wata kasa.

Dan wasan mai tsaron baya, ya buga tamaula karkashin David Moyes a lokacin da ya horar da Manchester United.

Evra ya bar Old Trafford ya koma Juventus da murza-leda a shekarar 2014, bayan da ya yi shekara uku a Italiya ne ya koma Marseille a Janairun 2017.

Dan kwallon ya buga wa United wasa 379 tsakanin shekarar 2006 zuwa 2014, inda ya lashe manyn kofi tara ciki har da Premier League da na Zakarun Turai a shekarar 2008.