Courtois zai tsawaita zamansa a Chelsea

Chelsea Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Courtois ya yi shekara uku a Real Madrid, kuma Real Madrid na son zawarcinsa

Mai tsaron ragar Chelsea, Thibaut Courtois zai tattauna da mahukuntan kungiyar kan tsawaita yarjejeniyarsa a Stamford Bridge, duk da ya ce zuciyarsa tana birnin Madrid.

Dan wasan mai shekara 25, wanda aka ce Real Madrid na son yin zawarci a badi, yana da kwantiragin da zai kare a Chelsea a karshen kakar badi.

Sai dai dan kwallon ya ce abu ne mai wahala ya kasa amsa kira zuwa Spaniya da taka-leda, bayan da ya yi shekara uku a Atletico Madrid, kuma 'ya 'yansa suna can da zama.

Courtois ya ce zai gana da mahukuntan Chelsea a watan Fabrairu kan tsawaita zamansa a Stamford Bridge, bayan da kungiyar ke fuskantar matsaloli da take son shawo kai a Janairu.

'Yan wasan Chelsea na yin hutun atisayen kwana uku, inda za su koma fagen fama a ranar Juma'a domin shirin tunkarar gasar Premier da West Brom a ranar 12 ga watan Fabrairu.

Labarai masu alaka