Sanchez ya amince da daurin gyara halinka

Man United Hakkin mallakar hoto Alex Morton
Image caption Sanchez ya koma Manchester United a watan Janairu, inda Mkhitaryan ya kom Gunners daga Old Trafford

Sabon dan wasan Manchester United, Alexis Sanchez ya amince da daurin jeka ka gyara halinka na wata 16, don kada a gurfanar da shi a gaban kuliya kan laifin kin biyan haraji.

Tsohon dan wasan Barcelonan na fuskantar gurfana a gaban kuliya kan laifin kin biyan haraji da ya kai fam 886,000.

Dan wasan ya samu kudaden da ake tuhumar ya ki biyan haraji a kansu ne, a wajen tallace-tallatace a tsakanin shekarar 2012 zuwa 2013.

Sanchez yana daya daga cikin manyan 'yan wasan da suka shiga ragar mahukuntan Spaniya kan kin biyan haraji.

A watan jiya sai da dan kwallon Real Madrid, Luka Modric, ya biya harajin kusan Yuro miliyan daya da aka tuhume shi.

Dan wasan Barcelona, Lionel Messi, da na Real Madrid Cristiano Ronaldo, duk sun fuskanci tuhumar kin biyan haraji a Spaniya.

Labarai masu alaka