'Yan Madrid 19 da za su kara da Sociedad

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Real tan ta hudu a kan teburin La Liga da maki 39

Kocin Real Madrid, Zinedine Zidane ya bayyana 'yan wasa 19 da za su fuskanci Real Sociedad a gasar La Liga wasan mako na 23 da za su kece-raini a Santiago Bernabeu a ranar Asabar.

A wasan farko a gasar bana da suka fafata a ranar 17 ga watan Stumbar 2017, Real ce ta ci 3-1.

Real tana ta hudu a kan teburi da maki 39, ita kuwa Sociedad makinta 26 tana ta 14 a kan teburin.

Ga jerin 'yan wasan da za su kara da Sociedad

Masu tsaron raga: Navas da Casilla da kuma Luca.

Masu tsaron baya: Carvajal da Ramos da Varane da Nacho da Marcelo da kuma Achraf.

Masu wasan tsakiya: Kroos da Modric da Casemiro da Asensio da Isco da kuma Kovacic.

Masu cin kwallo: Cristiano Ronaldo da Benzema da Bale da kuma Lucas Vazquez.