Watakila Dembele ya buga karawa da Getafe

Barcelona

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Barcelona tana mataki na daya a kan teburin La Liga

Bayan da Barcelona ta kai wasan karshe a Copa del Rey, za ta karbi bakuncin Getafe a wasan mako na 23 a gasar La Liga a ranar Lahadi a Nou Camp.

Barca na fatan kafa tarihin yin wasa na 22 a jere a La Liga ba tare da an doke ta ba a fafatawar shekarar nan.

Sai dai kungiyar ba za ta fuskanci Getafe da dan wasanta Samuel Umtiti wanda aka dakatar da Thomas Vermaelen ba.

Haka kuma kocin Barcelona, Ernesto Valverde bai gayyaci dan wasa Denis Suarez da kuma Andre Gomes cikin wadanda za su kece raini a ranar Lahadin ba.

Sai dai kocin ya gayyaci Ousmane Dembele cikin 'yan wasa 18 da za su fafata da Getafe a ranar Lahadin, bayan da ya warke daga rauninda ya yi jinya.

Ga 'yan wasan da za su kara da Getafe

Ter Stegen da Semedo da Pique da Rakitic da Sergio da Iniesta da Suarez da Dembele da Cillessen da Coutinho da Paulinho da kuma Messi.

Sauran sun hada da Paco Alcacer da Jordi Alba da Digne da Roberto da Aleix Vidal da kuma Yerry Mina.