AC Milan ta gwada wa SPAL kwanji

Serie A

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

AC Milan za ta karbi bakuncin Sampdoria a wasan mako na 25

AC Milan ta doke SPAL da ci 4-0 a gasar Serie A wasan mako na 24 da suka kara a ranar Asabar a filin wasa na Paolo Mazza.

Minti biyu da fara wasa Patrick Cutrone ya ci kwallon farko, kuma haka aka tafi hutun rabin lokaci AC Milan nada kwallo daya a raga.

Bayan da aka dawo daga hutu ne Patrick Cutrone ya kara na biyu kuma na 12 da ya ci a gasar Serie A ta bana.

Lucas Biglia ne ya ci kwallo na uku kuma daf da za a tashi daga wasan ne Fabio Borini ya ci na uku.

Da wannan sakamakon AC Milan tana ta bakwai a kan teburi da maki 38, za kuma ta karbi bakuncin Sampdori a ranar 18 ga watan Fabrairu.