Batshuayi ya kara ci wa Dortmund kwallo

Chelsea

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Batshuayi na buga wa Dortmund wasannin aro zuwa karshen kakar bana

Michy Batshuayi ya kara ci wa Borussia Dortmund kwallo a wasa na biyu da ya buga a gasar Bundesligar Jamus a ranar Asabar.

Dortmund ta yi nasarar cin Hamburg 2-0 a wasan mako na 22 da suka kece-raini a filin wasanta.

Batshuayi ne ya fara cin kwallo daf da za a je hutu kuma guda uku kenan da ya zura a raga a wasa biyu da ya yi wa Dortmund, daga baya Mario Gotze ya ci na biyu a fafatawar.

Wasu sakamakon wasannin da aka yi a ranar Asabar, Eintracht Frankfurt ta ci Cologne 4-2, Bayer Leverkusen ta yi rashin nasara a gida da ci 2-0 a hannun Hertha Berlin.

Hoffenheim kuwa 4-2 ta ci Mainz, yayin da Hannover ta yi nasarar doke Freiburg 2-1.