Man City ta sharara wa Leicester kwallaye

Asalin hoton, Getty Images
Sergio Aguero ya ci kwallo 20 a Premier shekarar nan
Manchester City ta yi nasarar doke Leicester 5-1 a wasan mako na 27 da suka kara a ranar Asabar a Ettihad.
City ce ta fara cin kwallo ta hannun Raheem Sterling minti uku da fara tamaula, sai dai minti 20 tsakani Jamie Jardy ya farke.
Bayan da aka dawo daga hutu ne Sergio Aguero ya ci wa City kwallo na biyu, da na uku da na hudu da na biyar, jumulla ya ci hudu rigis a wasan kuma guda 21 a Premier shekarar nan.
Da wannan sakamakon City ta ci wasa 23 ta yi canjaras a karawa daya Liverpool ta ci ta wasa daya a wasanni 27 da ta yi a bana, tana nan a matakinta na daya a kan teburri.
Manchester City za ta ziyarci Basel a gasar cin kofin Zakarun Turai a wasanta na gaba, ita kuwa Leicester City za ta karbi bakuncin Sheffield United a kofin FA.