Damben Bahagon Sisco da Dan Aminun Langa-Langa

Damben Bahagon Sisco da Dan Aminun Langa-Langa

Dambe tara aka yi a safiyar Lahadi a unguwar Dei-Dei a gidan wasa na Ali Zuma da ke Abuja, Nigeria.

Mohammed Abdu ne ya hada mana rahoton

An fara da wasan Dogon Dogon Washa Guramada da Shagon Dogon Auta daga Kudu babu kisa a turmi biyu da suka yi, sai wasan da Shagon Bahagon Dan Kanawa daga Kudu da ya kashe Tetenus din Na Bacirawa daga Arewa.

Sai wasan da aka yi canjaras tsakanin Bahagon Dan Sama'ila dag Kudu da Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa, shi kuwa Dogon Washa Guramada ya buge Dogon Minista a turmin farko.

Dambe tsakanin Garkuwan Mutanen Karmu daga Arewa da Shagon Bahagon Kanawa daga Kudu babu kisa, shi ma wasa tsakanin Shagon Samsu daga Arewa da Bahagon Dan Sama'ila daga Kudu babu wanda ya dafa kasa.

Dambe tsakanin Nuran Dogon Sani daga Arewa da Garkuwan Shagon Alabo daga Kudu turmi biyu suka yi babu kisa, sai karawar da Dogon Minsta daga Kudu ya shimfidar da Bahagon Ummaru Gundumi Guramada a turmin farko.

Daga karshe aka rufe fili da wasan da aka yi turmi biyu babu kisa tsakanin Dan Aminun Langa-Langa daga Arewa da Bahagon Sisco daga Kudu.