'Mourinho ba zai bai wa Real De Gea ba'

United

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Manchester United tana ta biyu a kan teburin Premier

Kocin Manchester United, Jose Mourinho ya sanar wa da Real Madrid cewar mai tsaron ragar United, David de Gea, mai shekara 27, ba zai bar Old Trafford ba in ji jaridar Sunday Mirror.

Liverpool da Arsenal na son sayen dan wasan tawagar kwallon kafar Ingila da Stoke City, Jack Butland kan fam miliyan 40, in ji The Sun.

Ita kuwa Telegraph cewa ta yi Chelsea tana son ta raba gari da Antonio Conte a karshen kakar shekarar nan cikin ruwan sanyi, ba wai ta koreshi ba.

Everton na son daukar kocin Shakhtar Donetsk, Paulo Fonseca domin ya maye gurbin Sam Allardyce a karshen kakar bana in ji Mail.

Mirror kuwa ta wallafa cewar Manchester City ta amince ta dauki dan kwallon Shakhtar Doneetsk dan Brazil, Fred kan fam miliyan 50.

Dan wasan Manchester City, Kevin de Bryne mai shekara 26, zai ci gaba da wasa a Ettihad har zuwa karshen kakar 2023, sannan ya koma buga gasar Amurka in ji mai kula da wasansa kuma The Sun ta wallafa.