Mourinho ya sha kashi a St James Park

United

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Karo na biyar kenan da aka ci United a gasar Premier ta bana

Newcastle United ta ci Manchester United 1-0 a wasan mako na 27 a gasar cin kofin Premier da suka kara a St James Park a ranar Lahadi.

Matt Ritchie ne ya ci kwallon bayan da aka koma zagaye na biyu a wasan.

Wannan nasara ya sa Newcastle United ta koma ta 13 ta fice daga 'yan ukun karshen teburin Premier ta kuma hada maki 28.

Wannan ne karo na biyar da aka ci United a gasar bana, bayan da ta yi canjaras biyar ta ci fafatawa 17.

Manchester United tana nan a matakinta na biyu da maki 56, za kuma ta karbi bakuncin Chelsea a ranar 25 ga watan Janairu a wasan mako na 28 a gasar ta Premier.