Ina shan wahalar rokon a sayo 'yan wasa — Conte

Chelsea Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Chelsea tana ta biyar a kan teburi da makinta 50

Kocin Chelsea, Antonio Conte, ya ce yana shiga tsaka mai wuya wajen shawo kan mahukuntan kungiyar su sayo sababbin 'yan wasa.

Chelsea, mai rike da kofin Premier, ta kasa sayo fitattun 'yan kwallo a lokacin da kasuwar musayar 'yan wasa ta Turai ta ci a watan Janairu.

Conte ya ce wani lokaci yana tattaunawa da wasu masu horar da tamaula wadanda suka kware wajen shawo kan kungiyoyinsu kan fitar da makudan kudin sayo 'yan wasa.

Kocin ya kuma ce yana zaune lafiya tare da Roman Abramovich, sannan ya kara da cewa ba gaskiya ba ne cewa dangantakarsu ta yi tsami.

Chelsea ta sha kashi da ci 4-1 a Watford a gasar Premier, za kuma ta karbi bakuncin West Brom a wasan mako na 27 na gasar a ranar Litinin.