NFF ta nada sabbin kocin tawagoginta

Nigerian Football Hakkin mallakar hoto The NFF
Image caption Nadin da aka yi wa kocin tawagogin Nigeria ya fara aiki nan take.

Hukumar kwallon kafar Nigeria ta nada kocin da za su ja ragamar tawagogin kwallon kafar kasar, domin fuskanatar kalubalen da ke gabanta.

Sai dai kuma nadin bai shafi mai horar da Super Eagles da mai jan ragamar matan Nigeria 'yan shekara 20 da wanda ke horar da Flamingos wadanda suke da yarjejeniya da NFF ba.

Shugaban kwamitin tsare-tsare na hukumar, Alhaji Yusuf Ahmed Fresh ya ce an bi duk hanyar da ta dace wajen nada masu horarwar kuma sun fara aiki nan take.

Ga jerin koci da NFF ta nada don jan ragamar tawagoginta:

Super Eagles ta 'yan wasan gida da masu buga Olympic

Koci: Salisu Yusuf

Masu taimaka masa: Imama Amapakabo da Kennedy Boboye da Fidelis Ilechukwu da kuma Alloy Agu mai horar da masu tsaron raga.

'Yan shekara 20 maza Flying Eagles:

Koci: Paul Aigbogun

Masu taimaka masa: Abdullahi Maikaba da Abubakar Bala da Hassan Abdallah mai nemo 'yan wasa da kuma Suleiman Shuaibu mai horar da masu tsaron raga.

'Yan shekara 17 Maza Golden Eaglets

Koci: Manu Garba

Masu taimaka masa: Nduka Ugbade da Jolomi Atune Ali da Bunmi Haruna mai nemo 'yan wasa da kuma Abideen Baruwa Olatunji (mai horar da masu tsaron raga.

'Yan shekara 15 Future Eagles

Koci: Alala Danladi Nasidi

Masu taimaka masa: Haruna Usman 'Ilerika da Ahmed Lawal Dankoli da Patrick Bassey mai nemo 'yan wasa da kuma Ernest Salolome mai horar da masu tsaron raga.

U13 BOYS TEAM: Jolomi Atune Ali (Head Coach); Jude Agada; Abdullahi Umar Tyabo; Adewale Laloko (Scouting); Adeoye Onigbinde (Goalkeepers' Trainer)