WAFU CUP: Falcons ta sauka a Abidjan

Super Falcons Hakkin mallakar hoto The NFF
Image caption Nigeria ta dauki kofin nahiyar Afirka karo takwas

Tawagar kwallon kafar Nigeria ta mata wadda ake kira Super Falcons ta sauka a birnin Abidjan na Ivory Coast, domin fafatawa a gasar WAFU CUP da za a fara a ranar Laraba.

Sabon kocin da ya ja ragamar 'yan wasan shi ne Thomas Dennerby wanda Wemimo Mathew da kuma Maureen Madu za su taimaka masa wajen gudanar da aikin.

Super Falcons mai tarihin lashe kofin nahiyar Afirka karo takwas za ta fara wasa da Benin a ranar Alhamis, sannan ta kece-raini da Senegal ranar 17 ga watan Fabrairu da kuma Togo a ranar 19 ga watan.

Labarai masu alaka