Yanzu ne PSG ke tasowa — Cabani

French League Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption PSG tana ta daya a kan teburin gasar Faransa

Edison Cavani ya ce har yanzu Paris St Germain tana tasowa a fagen tamaula, bai kamata a saka buri a kanta a Gasar cin Kofin Zakaraun Turai ba.

PSG, wadda ke mataki na daya a kan teburin gasar Faransa, za ta ziyarci Real Madrid a wasan farko na zagaye na biyua a Gasar Cin Kofin Zakarun Turai ranar Laraba.

Cavani ya shaida wa Marca cewa bai zama dole sai sun lashe kofin na Zakarun Turai nan kusa ba saboda sun sayi sababbin 'yan wasa kuma fitattu.

Dan wasan ya ce karawar da za su yi a Bernabeu wani tsani ne da zai kara musu kwarin gwiwar da zai kai kungiyar mataki na gaba a wasanninta sannu a hankali.

A bara a irin wannan matakin PSG ta doke Barcelona 4-0 a wasan farko, amma Barca ta yi nasara a karawa ta biyu da ci 6-1 jimilla.

Labarai masu alaka