Copa del Rey: An tsayar da ranar wasan karshe

Barcelona Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Barcelona tana ta daya a kan teburi a gasar cin kofin La Liga

Hukumar kwallon kafar Spaniya ta tsayar da ranar 21 a ga watan Afirilu, domin buga wasan karshe a gasar Copa del Rey na bana.

A ranar Litinin hukumar ta sanar da fafatawar tsakanin Barcelona da Sevilla a filin wasa na Athletico Madrid mai cin 'yan kallo 67, 829.

Wannan ne karon farko da sabon filin Atletico zai karbi wasan karshe a Copa del Rey, kuma shi ne zai karbi bakuncin wasan karshe a gasar cin kofin Zakarun Turai ta 2019.

Barcelona mai tarihin lashe Copa del Rey ta taba yin wasa a sabon filin, inda ta tashi 1-1 a cikin watan Oktoba.