Rocchi ne zai busa wasan Real Madrid da PSG

Champions League Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wannan ne karo na biyar da Rochi zai hura wasan da Real Madrid ke buga wa

Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai ta nada Gianluca Rocchi a matsayin wanda zai alkalanci karawa tsakanin Real Madrid da PSG a Santiago Bernabeu a ranar Laraba.

Paris St Germain za ta ziyarci Real Madrid a wasan farko na zagaye na biyu a gasar cin Kofin Zakarun Turai ta shekarar nana.

Wannan ne karo na biyar da Rocchi zai yi alkalancin wasan Real Madrid, bayan da ya hura wasa uku a kofin Zakarun Turai da daya a Europa Super Cup.

Rocchi ya fara da alkalancin karawar da Real Madrid ta ci Apoel 5-2 a gasar cin kofin Zakarun Turai a kakar 2011/12.

Ya kuma ja ragamar wasan da Manchester City da Real Madrid suka tashi 1-1 a karawar cikin rukuni a gasar ta Zakarun Turai ta 2012/13.

Shi ne ya kuma hura wasan da Real Madrid ta ci Wolfsburg 2-0 a wasan daf da na kusa da karshe a dai gasar Zakarun Turan a 2015/16.

Rocchi shi ne ya hura wasan da Real Madrid ta ci Manchester United 2-1 a wasan Europa Super Cup a ranar 8 ga watan Augustan 2017.

Labarai masu alaka