'Yan Juventus 19 da za su kara da Tottenham

Champions League
Bayanan hoto,

Wannan ne karon farko da Juventus da Tottenham za su kara a tsakaninsu

Kocin Juventus, Massimiliano Allegri ya bayyana 'yan wasa 19 da za su karbi bakuncin Tottenham a gasar cin Kofin Zakarun Turai a ranar Talata.

Tottenham za ta ziyarci Italiya domin buga wasan farko a zagaye na biyu a gasar ta Zakatun Turai, kuma wannan ne karon farko da kungiyoyin biyu za su kece-raini a tsakaninsu.

A ranar 7 ga watan Maris ne Tottenham za ta karbi bakuncin wasa na biyu a Wembley.

Ga jerin 'yan wasan Juventus da za su kara da Tottenham:

 • Buffon
 • De Sciglio
 • Chiellini
 • Benatia
 • Pjanic
 • Khedira
 • Marchisio
 • Higuain
 • Douglas Costa
 • Alex Sandro
 • Pinsoglio
 • Mandzukic
 • Asamoah
 • Szczesny
 • Rugani
 • Sturaro
 • Bentancur
 • Bernardeschi
 • Muratore