Lacazaette zai yi jinyar mako shida

Arsenal Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Lacazette zai yi jinyar mako shida, bayan da aka yi masa aiki a gwiwarsa

Dan wasan Arsenal, Alexandre Lacazette zai yi jinyar mako shida bayan da likitoci suka yi masa aiki a gwiwar kafarsa a ranar Talata.

Dan kwallon mai shekara 26 ya buga karawar da Tottenham ta ci Arsenal 1-0 a gasar Premier inda ya barar da damar-maki.

Arsenal ta ce aikin da likitoci suka yi wa dan kwallon an yi shi cikin nasara, zai kuma dawo taka-leda tsakanin mako hudu zuwa shida.

Danny Welbeck ne kadai dan wasa mai cin kwallo da ya rage a karawar da Arsenal za ta yi da Ostersunds FK a gasar Europa a ranar Alhamis.

Sabon dan wasan da Arsenal ta saya a watan Janairu, Pierre-Emerick Aubameyang ba zai buga wa Arsenal gasar Europa ba.