Gasar Turai: Madrid ta yi wasa 18 ba a doke ta a gida ba

Champions League Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Real Madrid ta lashe kofin Zakarun Turai sau 12 a tarihi

Real Madrid ta yi nasarar cin Paris St Germain 3-1 a wasan farko na zagaye na biyu a Gasar Cin Kofin Zakarun Turai da su kara a Santiago Bernabeu a ranar Laraba.

Da wannan sakamakon Real Madrid ta yi wasa 18 a gasar ta Zakarun Turai a gida ba tare da an doke ta ba, inda ta yi nasarar cin wasa 15 da canajaras uku, ta kuma ci kwallo 50 aka zura mata 12 a raga.

Rabon da Real ta yi rashin nasara a gida a gasar ta Zakarun Turai tun a wasan zagaye na biyu bayan da Schlke ta yi nasara da ci 4-3 a kakar 2014/15.

Manyan kungiyoyin Turai sun sha kashi a karawa da Madrid a gasar a Bernabeu da suka hada da PSG da Manchester City da Borussia Dortmund da kuma Bayern Munich da sauransu.

Ko a gasar bana, Real ta ci Apoel 3-0 ta kuma tashi 1-1 da Tottenham, sannan ta ci Borussia Dortmund 3-2 a wasannin cikin rukuni da ta yi a gidanta.

Labarai masu alaka