Manchester City ta sharara wa Basel kwallaye

Champions League Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Basel za ta ziyarci Ettihad a wasa na biyu a cikin watan Maris

Basel ta yi rashin nasara a gida a hannun Manchester City, bayan da aka doke ta da ci 4-0 a wasan farko a zagaye na biyu a gasar cin kofin zakarun Turai da suka kara ranar Talata.

City ta ci kwallayen ne ta hannun Ilkay Gundogan wanda ya ci biyu a karawar sai Bernardo Silva da Sergio Aguero suka ci dai-dai kowannensu.

Dan wasan City, Leroy Sane ya buga karawar, wanda aka yi tsammanin zai yi jinyar mako shida, bayan da ya yi rauni a Cardiff a gasar kofin FA a ranar 28 ga watan Janairu.

Manchester City za ta karbi bakuncin Basel a wasa na biyu a ranar 7 ga watan Maris din 2018.