Kwallo hudu aka ci a wasan Juventus da Tootenham

Champios League Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Juventus za ta ziyarci Wembley a wasa na biyu ranar 7 ga watan Maris

Kungiyar Juventus ta tashi wasa 2-2 da Tottenham a wasan farko na zagaye na biyu a Gasar Cin Kofin Zakarun Turai da suka kara a ranar Talata a Italiya.

Juventus ce ta fara cin kwallo ta hannun Gonzalo Higuain minti biyu da fara tamaula, sannan minti bakwai tsakani ya ci ta biyu a bugun fenariti.

Saura minti 10 a tafi hutu ne Tottenham ta zare kwallo daya ta hannun Harry Kane, sannan Christian Eriksen ya ci na biyu a bugun tazara, bayan da aka koma wasan zagaye na biyu.

Tottenham za ta karbi bakuncin Juventus a wasa na biyu a ranar 7 ga watan Maris din 2018.

Labarai masu alaka