Real Madrid ta samu kwarin gwiwa a kan PSG

Champions League Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Real Madrid za ta ziyarci Faransa a wasa na biyu a ranar 6 ga watan Maris

Real Madrid ta ci Paris St Germain 3-1 a Gasar Cin Kofin Zakarun Turai da suka kara a ranar Laraba a Santiago Bernabeu.

PSG ce ta fara cin kwallo ta hannun Adrien Rabiot a minti na 33 da fara tamaula, kuma daf da za a tafi hutu Madrid ta farke ta hannun Cristiano Ronaldo a bugun fenariti.

Saura minti bakwai a tashi daga wasan Cristiano Ronaldo ya ci na biyu, sanan Marcelo Vieira Da Silva ya kara na uku a raga.

Real da PSG sun kara a gasar cin kofin Zakarun Turai a kakar 2015/16, inda suka tashi canjaras a Faransa a wasan farko a ranar 21 ga watan Oktoba, a wasa na biyu a ranar 3 ga watan Nuwamba Real ta ci 1-0 a Spaniya.

PSG zata karbi bakuncin Real Madrid a wasa na biyu a ranar 6 ga watan Maris din 2018.

Ga jerin 'yan wasan PSG da suka fuskanci Real Madrid:

 1. Alphonse Areola
 2. Yuri Berchiche
 3. Edinson Cavani
 4. Dani Alaves
 5. Angel di Maria
 6. Lassana Diarra
 7. Julian Draxler
 8. Presnel Kimpembe
 9. Layvin Kurzawa
 10. Giovani Lo Celso
 11. Marquinhos
 12. Kylian Mbappe
 13. Thomas Meunier
 14. Neymar Junior
 15. Javier Pastore
 16. Adrien Rabiot
 17. Thiago Silva
 18. Kevin Trapp
 19. Marco Verratti

Labarai masu alaka