''Zidane bai damu da makomarsa a Real ba''

Champions League Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Zidane ya maye gurbin Rafael Benitez a watan Janairun 2016

Kocin Real Madrid, Zinedine Zidane ya ce baya tunanin makomarsa a Real Madrid tun kafin karawar da kungiyar za ta yi da PSG.

Real Madrid za ta karbi bakuncin Paris St Germain a wasan farko na zagaye na biyu a gasar cin Kofin Zakarun Turai a ranar Laraba.

A bara ne Real ta lashe kofin Zakarun Turai na 12, kuma ta zama ta farko da ta ci kofin karo biyu a jere tun bayan shekarar 2012.

Zidane na fuskantar kalubale, bayan da aka fitar da Madrid a gasar Copa del Rey, sannan tana ta hudu a kan teburin gasar La Liga ta bana.

Kocin ya ce kullum sai kayi fama da kalubale a Bernabeu, saboda haka zai ci gaba da bayar da gudunmawa kamar yadda yake yi.

Real za ta karbi bakuncin PSG da karfin gwiwa, bayan da ta ci Real Sociedad 5-2 a karshen mako, inda Ronaldo ya ci uku a karawar.

Labarai masu alaka