Europa: Tazara tsakanin Arsenal da Ostersund

Europa Cup
Bayanan hoto,

Wannan ne karon farko da kungiyoyin biyu za su kece-raini a tsakaninsu

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal za ta ziyarci Sweden domin karawa da Ostersund a wasan farko na zagaye na biyu a gasar Europa Cup a ranar Alhamis.

Babu yadda za a hada kwarewar Arsenal da Ostersund a fagen tamaula, to amma a filin wasa ne za a bambamci gwani a tsakaninsu.

An kafa Ostersund a shekarar Arsene Wenger ya zama kocin Arsenal.

Ga bambamcin dake tsakanin Ostersund da Arsenal:

Shekarar da aka kafa kungiya:

Ostersund: 1996

Arsenal: 1886

Lashe lambobin yabo:

Ostersund: Guda 2 - Division One Northern da kuma Svenska Cupen

Arsenal: Guda 45 - Rukunin farko/Premier League 13 da FA Cup 13 da League Cup 2 da Cup Winners' Cup da Inter-Cities Fairs Cup da kuma Community Shield 15.

Yawan 'yan kallo a filin wasa:

Ostersund: Jamtkraft Arena - 8,466

Arsenal: Emirates Stadium - 59,867

Dan wasa mai tsada da kungiya ta saya:

Ostersund: Saman Ghoddos - Fam 68,000 daga Syrianska a watan Janairun 2016

Arsenal: Pierre-Emerick Aubameyang - Fam miliyan 55 daga Borussia Dortmund a Janairun 2018