Liverppol ta sharara wa Porto kwallaye

Champions League
Bayanan hoto,

Liverpool ta ci kwallo 28 a gasar cin kofin zakarun Turai ta bana

FC Porto ta yi rashin nasara a gida a hannun Liverpool da ci 5-0 a wasan farko na zagaye na biyu a gasar cin kofin Zakarun Turai da suka kara a ranar Laraba.

Liverpool ta fara cin kwallo ta hannun Sadio Mane a minti na 25 da fara wasa, sannan minti hudu tsakani Mohamed Salah ya kara na biyu.

Bayan da aka dawo daga hutu ne Sadio Mane ya ci na uku da wadda Roberto Firmino ya ci na hudu sai Sadio Mane ya kara na biyar na uku rigis da ya ci a karawar.

Liverpool ta ci kwallo 28 a gasar Zakarun Turai ta bana, inda ta ci 23 a wasannin cikin rukuni.

Liverpool za ta karbi bakunci FC a wasa na biyu a ranar 6 ga watan Maris din 2018 a Anfield.