Luwadi: An samu tsohon kocin Man City Bennell da karin laifuka

Barry Bennell Hakkin mallakar hoto Others
Image caption Tsohon kociyan ya rika lalata da yara maza 'yan shekara 8 zuwa 15 da ke karkashinsa

An samu tsohon kocin kwallon kafa na matasa Barry Bennell da laifuka bakwai na lalata da yara maza, bayan daman tun a baya an yanke masa hukuncin zaman yari a Birtaniya da Amurka.

A ranar Talata ne aka samu Bennell mai shekara 64 wanda ya yi aiki da kungiyoyin matasa na Crewe Alexandra da Manchester City a shekarun 1980 da laifi 36 na lalata da matasan 'yan kwallo.

Ayarin masu taimaka wa alkali yanke hukunci a kotun Crown Court ta Liverpool ya same shi da karin tuhuma bakwai.

An sheda wa masu taimaka wa alkalin cewa tsohon kociyan ya kasance da iko kan 'yan wasa masu shekara takwas zuwa 15, kuma ya yi amfani da wannan dama wajen muzguna musu ta hanyar lalata.

Saboda rashin lafiya da yake fama da shi, Bennell, wanda yanzu ake kiransa da suna Richard Jones ya bayyana ne a kotun ta hanyar hoton bidiyo a tsawon mako biyar na shari'ar.

Wannan shi ne karo na hudu da ake samun Bennell da laifin lalata da yara.

Tun a baya an sheda wa masu taimaka wa alkalin cewa an yanke wa tsohon kociyan hukuncin zaman gidan yari uku a Birtaniya da Amurka.