Kila Aaron Ramsey ba zai buga wasan karshe na Carabao ba - Wenger

Aaron Ramsey Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Aaron Ramsey ya ci kwallonsa uku rigis a wasa daya ne a karon farko lokacin da Arsenal ta doke Everton

Kociyan Arsenal Arsene Wenger ya ce kila dan wasansu na tsakiya na Wales Aaron Ramsey ba zai buga wasan karshe da za su yi ba na cin kofin (EFL) Carabao, da Manchester City ranar Lahadi, 25 ga watan Fabrairu.

Ramsey, wanda ya ci kwallonsa uku rigis a karon farko a wasan da ya yi wa Arsenal na karshe, lokacin da ta doke Everton 5-1, bai taka leda ba a karawar hamayya ta Arewacin Landan wadda Tottenham ta casa su.

Wenger ya ce raunin da Ramsey ke jinya yana da hadari, saboda haka ne ma ba a tafi da shi ba wasansu na kofin Europa da za su yi ranar Alhamis da Ostersunds.

Kociyan ya kara bayani da cewa, suna tsammanin dan wasan ya kara murmurewa a raunin matse-matsin da ya ji, saboda har zuwa yanzu ba ya gudu sosai kamar yadda suke son ganin yana yi

Ramsey ne ya ci bala-balan da suka ba Arsenal nasara a wasanninta na karshe na cin kofin FA a 2014 da 2017.