Sunday Oliseh ya yi karya in ji kungiyarsa Fortuna Sittard

Sunday Oliseh da 'yan wasan kungiyar Fortuna Sittard Hakkin mallakar hoto AFP/Getty
Image caption Sunday Oliseh ya kama aikin horar da kungiyar Fortuna Sittard ta rukuni na biyu a Holland a watan Disamba na 2016

Kungiyar Fortuna Sittard da ke rukuni na biyu a Holland ta musanta zargin da Sunday Oliseh ya yi na cewa ya ki yarda a aikata wasu abubuwa da suka saba ka'ida ne shi ya sa ta dakatar da shi daga aikin kociya.

A ranar Laraba ne kungiyar wadda ke wasa a rukuni na biyu ta dakatar da tsohon kyaftin din na Najeriya, a kan abin da ta kira ayyukan da ba za ta lamunta da su ba.

A martanin da ya mayar Oliseh ya ce kungiyar tana son ya saba doka ne.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar ranar Alhamis din nan ta ce tana karbar shawarwarin shari'a domin duba yadda za ta kori kociyan.

A sanarwar kungiyar ta ce za ta gabatar da maganar gaban hukumar kwallon kafa ta Holland, wadda mai zaman kanta ce, wadda za ta duba ta ga ko akwai isassun dalilan da za su sa kungiyar soke kwangilar aiki da kociyan.

A watan Disamba na 2016 kungiyar Sittard ta nada Oliseh a matsayin kociyanta.

A kakar da ta wuce kungiyar ta gama a matsayi na 17 a gasar mai kungiyoyi 20, amma a yanzu tana matsayi na uku a tebur, kuma maki biyar ne tsakaninta da ta daya NEC.