Kofin Europa: Arsenal ta doke Ostersunds 3-0

Nacho Monreal na muranr cin Ostersunds FK

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Bal din da Nacho Monreal ya fara ci ta sa yana da hannu a kwallo biyar da Arsenal ta ci a wasansa shida na karshe da ya yi wa kungiyar

Arsenal ta kama hanyar samun gurbi a matakin kungiyoyi 16 na cin kofin Turai na Europa bayan da ta doke mai masaukinta kungiyar Ostersunds FK ta Sweden 3-0 a ranar Alhamis din nan.

A wasan wanda shi ne karo na farko dan bayan Arsenal Nacho Monreal ne ya fara daga raga a minti na 13, bayan da mai tsaron ragar Ostersund Aly Keita ya yi aman wata bal da Alex Iwobi ya sheka masa.

Sai kuma a minti na 24 inda dan bayan kungiyar ta Sweden, Sotirios Papagiannopoulos ya kuskure ya ci kansu bayan da Henrikh Mkhitaryan ya cillo wata bal daga gefe.

'Yan Ostersund din sun dan farfado bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci, amma kuma Mesut Ozil ya kara kwantar da su da ci na uku a minti na 58.

Masu gidan sun samu damar cin ladan gabe, da fanareti amma kuma golan Arsenal, David Ospina ya haramta musu, ya kama kwallon.

A ranar Alhamis mai zuwa 22 ga watan nan na Fabrairu Arsenal za ta karbi bakuncin kungiyar ta Sweden wadda Graham Potter dan Ingila ke yi wa kociya, a karawa ta biyu, a filin Emirates, da karfe (9:05 na dare agogon Najeriya da Nijar).

Ga sakamakon wasu daga cikin wasannin na Europa 15 na Alhamis din

Olympique Marseille 3 - 0 Sporting Braga

Ludogorets 0 - 3 Milan

Real Sociedad 2 - 2 Salzburg

Spartak Moskva 1 - 3 Athletic Club

Nice 2 - 3 Lokomotiv Moskva

Borussia Dortmund 3 - 2 Atalanta

Astana1 - 3 Sporting CP

København 1 - 4 Atlético Madrid

Celtic 1 - 0 Zenit

Napoli 1 - 2 RB Leipzig

Olympique Lyonnais 3 - 1 Villarreal

Partizan1 - 1 Viktoria Plzeň