Arsenal na son sayen Werner na RB Leipzig

Arsenal Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption The Sun ta ce Chelsea da Liverpool da Manchester United na son sayen Werner

Arsenal na son sayen dan wasan RB Leipzig, mai cin kwallo Timo Werner, mai shekara 21 dan kasar Jamus in ji jaridar The Sun.

Jaridar ta wallafa cewar Chelsea da Liverpool da Manchester United sun taya dan wasan kan fam miliyan 50, inda kungiyar Jamus bata sallamar ba.

Mail kuwa cewa ta yi Arsene Wenger na shirin daukar dan wasan Lyon mai wasan tsakiya, Nabil Fekir kuma shi ne na farko da zai fara kai wa Gunners, zai iya biyan fam miliyan 45 domin a dauki dan kwallon Faransa mai shekara 24.

Liverpool na bibiyar dan kwallon Tottenham, Victor Wanyama, bayan da Emre Can ba shi da makoma a Anfield in ji Mail.

The Sun ta ce aikin Alan Pardew na tangal-tangal, lokacin da 'yan wasan West Brom hudu suka nemi gafara, bayan da aka sace taksi a wajen dakin abinci a Barcelona a ranar Alhamis.

Telegraph ta wallafa cewar kocin Manchester City, Pep Guardiola ya ce kungiyar bata aikata laifi ba a lokacin da ta kasa sayen dan wasan Leicester City, Riyad Mahrez a watan Janairu.

Manchester United na son sayen dan kwallon Nice, Jean Michael dan kasar Ivory Coast, wanda kunshin yarjejeniyarsa ya tanadi kudin sayar da shi fam miliyan 33 in ji Mail.

Labarai masu alaka