Pogba bai buga karawa da Huddersfield ba

Man United Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption United ce za ta ziyarci Huddersfield a kofin FA wasan zagaye na biyar

Paul Pogba bai buga karawar da Manchester United ta doke Huddersfield 2-0 a gasar kofin FA a ranar Asabar ba., sakamakon rashin lafiya da yake fama.

United ta maye gurbin Pogba da dan wasan matasan kungiyarta, Ethan Hamilton mai shekara 19.

Shi kuwa Erik Bailly ya murmure, bayan jinyar wata uku da ya yi sakamakon aiki da likitoci suka yi masa a kafarsa, har ma ya canji Lukaku a fafatawar

Sai dai kuma Ander Herrera da Marcus Rashford ba su buga fafatawar ba, sakamakon jinya da suke yi.

Wannan ne karo na biyu da United ta doke Huddersfield a kakar bana, ta kuma kai zagaye na shida a gasar ta FA.

Labarai masu alaka