Real Madrid za ta yi wasa hudu a kwana 10

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Real tana ta hudu a kan teburin La Liga, za kuma ta ziyarci Real Betis a ranar Lahadi

Real Madrid za ta buga wasan gasar La Liga hudu a kwana 10, bayan da kungiyar take ta hudu a kan teburin bana.

A ranar Laraba Real ta ci Paris St Germain 3-1 a wasan farko na zagaye na biyu a gasar cin kofin zakarun Turai, za kuma ta mai da hankali kan La Liga domin ta samu gurbin shiga gasar badi.

Real za ta fara ziyartar Real Betis a wasan mako na 24 a ranar Lahadi, kungiyar da ta doke Madrid 1-0 a watan Satumba a Santiago Bernabeu.

Kwana uku tsakani Real za ta ziyarci Leganes a wasan mako na 25, daga nan Madrid ta karbi bakuncin Alaves a Bernabeu a ranar 24 ga watan Fabrairu a wasan mako na 26.

Wasa na hudu cikin kwana 10 da Madrid za ta yi shi ne na mako 27, wanda za ta ziyarci Espanyol, duk da cewar kila wasan Espanyol da Alaves na kasan teburi, amma za ta yi gumurzu a fafatawa da Betis da Leganes domin suna kan ganiyarsu.

Daga nan ne Real za ta yi hutun mako daya sannan ta karbi bakuncin Getafe a Bernabeu, kwanaki uku tsakani ta ziyarci Faransa domin karawa da PSG a wasa na biyu a gasar cin kofin zakarun Turai.

Labarai masu alaka